Sanata Joshua Dariye, Tsohon Gwamnan Jihar Filato
Sanata Joshua Dariye, Tsohon Gwamnan Jihar Filato

Rahotanni na cewa, yanzu haka an dauke tsohon gwamnan jihar Filato Sanata Joshua Dariye daga gidan yari zuwa wani asibiti bayan ya kamu da cutar gazawar koda.

Wata majiya ta ce an kwashi Dariye ne zuwa asibitin koyarwa da ke Gwagwalada a Abuja tun a watan Disamban da ya gabata.

Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta Nijeriya reshen Birnin Tarayya Abuja Chukwuedo Humphrey, ya tabbatar da cewa Dariye ya na asibiti, amma ya ki bayyana yanayin ciwon da ya ke damun shi.