Matar Shugaban Kungiyar ‘yan jarida na Jihar Nasarawa Suleiman Abubakar ta samu kubuta tare da sauran mata uku da aka yi garkuwa da su.

An dai yi garkuwa da mutanen ne a makon da ya gabata, a kan hanyar su ta komawa Lafiya daga Keffi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Nasarawa Sama’ila Juma’a a Lafiya cewa masu garkuwar sun sako matan da misalign karfe 9:45 na daren Alhamis da ta gabata.

Ya ce masu garkuwar sun saki matan ne saboda matsin lambar bincike da neman su da jami’an tsaro su ka rika yi.

Ya ce dukkan matar da aka kamac din, sun je yin rajistar aikin bautar kasa ne a sansanin NYSC da ke Keffi, Jihar Nasarawa.

Ya ce tuni kowace ta koma gida cikin iyalan ta.

Sai dai Shugaban Kungiyar ’Yan Jaridar ya shaida wa manema labarai cewa, sai da ya biya kudi kafin a saki matar sa.

Leave a Reply