Maharan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, sun sako ƙarin mutane bakwai daga cikin fasinjojin da su ka sace a watan Maris.

Mai shiga tsakani a sasantawa da maharan da dangin fasinjojin Malam Tukur Mamu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Fasinjojin da aka sako dai sun hada da mata biyu da namiji daya da kuma yara hudu.

Sanarwar ta ce, Sheikh Ahmad Gumi ne ya shiga tsakani a wannan karon, tun bayan bayyanar wani bidiyo makonni biyu da su ka gabata, wanda ke nuna yadda maharan ke azabtar da fasinjojin.

Ya ce Sheikh Ahmad Gumi ya tuntuɓi maharan ta hanyar mai ba shi shawara ta fuskar yaɗa labarai, inda ya roƙe su cewa su taimaka su sako yaran da iyayen su, kasancewar yaran ba su da lafiya kuma yanayin da su ke ciki ya na ƙara taɓarɓarewa tun bayan dukan da aka yi wa mahaifin su.

Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin ko an biya kuɗin fansa kafin a sako mutanen, amma rahotanni na cewa na baya da aka sako sun biya miliyoyin naira kafin su samu ‘yancin su.

Leave a Reply