Tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN Muhammad Sanusi Lamido II, ya ce sai da ya gargadi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari cewa manufofin ta na tattalin arziki za su lalata arzikin Nijeriya.
Muhammad Sanusi, ya kuma koka da halin da Nijeriya ke ciki, ya na mai cewa Nijeriya ba za ta samu cigaban da ya kamata ba muddin masu rike da mukaman gwamnati ba su dauki aikin su da kima ba.
Tsohon Sarkin ya bayyana haka ne, yayin wani muhimmin taro da ya gudana a Lagos game da tsarin tattalin arzikin Nijeriya, inda ya ce idan kowane shugaban kasa da gwamna da minista da kwamishina zai dauki aikin shi da muhimmanci, Nijeriya ba za ta kasance inda ta ke a yau ba.
Ya ce ya gargadi gwamnatin tarayya a kan illolin da ke tattare da manufofin ta a shekara ta 2015, musamman yadda za ta lalata tattalin arzikin Nijeriya.