Jam’iyyar APC ta bayyana shirin fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Satumba na shekara ta 2022.

An dai shirya gudanar da taron kwamitin ayyuka na kasa a karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, domin yanke shawara a kan ranar da kuma shirya taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na kasa.

Wata majiyar jam’iyyar ta ce, taron na gaugawa da majalisar zartarwa ta jam’iyyar za ta yi ya zama dole, domin a baya kwamitin ya sabunta ikon sa da aka mika wa kwamitin amintattu na jam’iyyar a karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu.

Bayan cikar kwanaki 90, wata majiya mai karfi ta shaida wa manema labarai cewa, kwamitin amintattun ba zai iya daukar muhimman shawarwari a madadin jam’iyyar ba tare da amincewar kwamitn majalisar zartarwar ba.

Leave a Reply