Wasu mahara sun yi garkuwa da matar Shugaban Kungiyar ‘yan jarida ta Jihar Nasarawa Suleiman Abubakar, tare da wasu mata uku a Karamar Hukumar Akwanga da ke Jihar Nasarawa.
An dai tare matar sa mai suna Yahanasu ne tare da sauran matan uku da misalign karfe 7 na dare, yayin da su ke kan hanyar tafiya tsakanin titin Gudi zuwa Gareku da ke cikin Karamar Hukumar Akwanga.
Suleiman ya ce, maharan sun tare motar da su ke ciki, sannan su ka bude mata wuta a lokacin da su ke komawa Lafiya daga Keffi, inda matar ta sa ta je yin rajistar shigar da sunan ta a Sansanin Masu Bautar Kasa NYSC.
Ya ce wutar da aka bude wa motar ta firgita direban, inda ya fada wani rami, nan da nan ‘yan bindigar su ka kewaye su.
Suleiman ya cigaba da cewa, an gudu da matar sa da matar wani tsohon dan majalisar dokoki ta Jihar Nasarawa, da wasu mata biyu da su ka kama a cikin wata mota ta daban.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Nasarawa Sama’ila Usman, ya ce an baza zaratan jami’an tsaro, wadanda tuni sun bazama aikin tabbatar da cewa sun ceto matan.



































