Kasafin Kudi: Dogara Ya Soki Lamirin Shugaba Buhari A Majalisa
Shugaban Majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya soki lamirin shugaba Buhari dangane da kiyasin kasafin shekara ta 2019 da ma na shekarun baya da ya gabatar a Majalisa.
Dogara ya yi kakkausar sukar ne a gaban jama’a, yayin da ya ke jawabin bude taron fara saurare da bin kadin abin da kasafin shekara ta 2019 ya kunsa.
Ya ce duk kasafin kudaden da shugaba Buhari ke kai wa Majalisa ana tsara su ne kawai domin biyan bukatar masu tsara kasafin kadai.
Yakubu Dogara ya kara da cewa, kasafin kudaden a ko da yaushe su kan karkace daga turbar da al’ummar Nijeriya za ta fi amfana da su.
Ya ce irin yadda ma’aikatu ke zaben ayyukan da za su yi, ya kan kauce daga ainihin abin da ya kamata, tare haifar da matsala wajen aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin.
Ya ce mahukuntan gwamnati da ma’aikatu sun fi karkata ne a inda su ke so a kashe kudaden kasafi, ba inda ya kamata ko ya fi cancanta a kashe kudaden ko a yi ayyukan ba.



































