Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi, ta sanya tukuicin naira
miliyan ɗaya ga duk wanda ya bada bayanan inda ɗan
majalisar wakilai na mazaɓar Bauchi Yakubu Shehu ya ke.

Ana dai neman ɗan majalisar ne ruwa a jallo kamar yadda
rundunar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar, bisa
zargin shi da laifin tada husuma da rikici da kuma kisan kai.

A cikin sanarwar, rundunar ‘yan sandan ta ce za ta bada
tukuicin naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya bada bayanin da
zai kai ga kama shi.

Yakubu Shehu dai ɗan jam’iyyar NNPP ne, wadda a cikin ta
ya yi takarar majalisar dattawa amma ya yi rashin nasara a
hannun Sanata Lawal Yahaya Gumau.

Leave a Reply