NAFDAC Raids Zaria Market, Seizes Expired Aphrodisiacs

Hukumar Kashe Gobara ta kasa, ta ayyana shirin ta na
kaddamar da tashoshin kashe gobara a kasuwannin da ke
fadin Nijeriya.

Shugaban Hukumar mai kula da shiyyar Kano da Jigawa
ACG Ahmed Garba-Karaye ya bayyana haka, lokacin da ya
ziyarci Kasuwar Singa domin duba irin barnar da gobara ta yi
a ranar Litinin d ta gabata.

Ahmed Garba-Karaye, ya ce hukumar ta himmatu wajen
dakile aukuwar gobara da kuma shawo a kan ta idan tsautsayi
ya sa ta auku, ya na mai jaddada cewa bincike ya kankama
domin nazari tare da tabbatar da bin ka’idojin kashe gobara a
gine-ginen jama’a.

Ya ce ana samun karuwar aukuwar gobara a kasuwannin
Kano ne sakamakon yanayin zafi da kuma rashin ingancin
kayayyakin lantarki, don haka ya kamata a rika rage cunkuso
domin samun wadatacciyar iska da za ta rika ratsawa a cikin
shaguna.

Leave a Reply