Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, ta ce kimanin jami’an
tsaro dubu 18 da 748 ne aka baza a fadin jihar, domin gudanar
da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi
ranar 18 ga watan Maris.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Mamman Dauda ya
bayyana haka, yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai
na Nijeriya a Kano, inda ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an
tsaro za su samar da tsaro mai inganci a fadin runfunan zabe
dubu 11 da 222 da ke unguwanni 484 a fadin kananan
hukumomi 44 na jihar.

Mamman Dauda ya kara da cewa, tuni an bada cikakken
umarnin gudanar da aiki ga kwamandojin kowanne yanki, da
jami’an ‘yan sanda na shiyya-shiyya domin aiwatar da su.

Kwamishinan ya kuma bada tabbacin cewa, ‘yan sanda da
sauran jami’an tsaro a shirye su ke domin kare masu kada
kuri’a da jami’an hukumar zabe a lokacin zabe da kuma bayan
zabe.