Gamayyar jam’iyyu 28 a Jihar Sokoto, sun bada sanarwar kin amincewa da nasarar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa dai ta bayyana cewa, gwamna Aminu Tambuwal ne ya yi nasara a kan dan takarar jam’iyyar APC da bambancin kuri’u 342 kacal.

Shugaban gamayyar jam’iyyun Musa Aiyu na jam’iyyar NEPP ne ya bayyana wa manema labarai matakin su na kin amincewa da sakamakon zaben.

Musa Aliyu, wanda shi ne dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar NEPP a Jihar Sokoto, ya ce an yi tashe-tashen hankula kuma an yi kumbiya-kumbiya a lokacin zaben, lamarin da ya ce hakan ya saba wa dokokin zabe da kuma dokar kasa.

Ya ce sun lura da cewa a zabubbukan da aka maimaita an yi cinikin kuri’u tare da razana jama’a, wasu wuraren ma ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ba.

Leave a Reply