Jam’iyyar APC a jihar Adamawa, ta yi barazanar kaurace wa zaben gwamna da za a maimaita a jihar.
Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC a jihar Adamawa Ahmed Lawan ya bayyana matsayar jam’iyyar da cewa, jam’iyyar ta nuna rashin amincewa da zaben kuma ta sanar da hukumar zabe matsayin ta.
Sai dai shugaban jam’iyyar PDP na jihar Adamawa Tahir Shehu, ya ce a shirye su ke domin gudanar da zaben.
Yayin da aka tuntubi kwamishinan zabe na jihar Kassim Gaidam, ya ce hukumar za ta gudanar da zaben kamar yadda ta shirya a ranar Alhamis, ya kuma bukaci dukkan jam’iyyun su yi aiki domin tabbatar da zaben ba tare da matsala ba.



































