Akalla mutane biyu sun rasa rayukan su, yayin da gidaje 38 su ka kone a wani rikicin kabilanci da ya barke a garin Andaha da ke hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.
Mazauna kauyuka uku da ke kusa da garin da rikicin ya faru sun kaurace wa gidajen su saboda tsoron kai harin daukar fansa a kan su.
Mutanen, sun fara kaurace wa gidajen su ne bayan samun rahoton kashe wata budurwa mai shekaru 19 da ake zargin wasu ‘yan ta’adda da aikatawa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Nasarawa Sama’ila Usman, ya tabbatar wa manema labarai afkuwar rikicin.
A cewar sa, rikicin ya samo asali ne bayan wasu ‘yan ta’adda sun yi wa wasu mata uku ‘yan kabilar Mada fyade yayin da su ke kan hanyar komawa gida daga wani biki da su ka halarta a garin Katanza.
Kakakin
ya ce, ‘yan ta’addan sun lakada wa daya daga cikin ‘yan matan mai suna Joy
Danlami duka, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ta.





































