Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta dakatar da shirin ba ‘yan takarar da su ka yi nasara a zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a jihar Zamfara shahadar nasarar cin zaben.

Wannan dai, ya biyo bayan wani umarni ne da hukumar ta ce ta samu daga wata babbar kotu a da ke Sokoto game da rikicin jam’iyyar APC da ke da alaka da yadda aka yi zaben fidda gwanin da su ka yi mata takara a jihar.

Hukumar zaben ta bayyana haka ne a shafin ta na Twitter, inda ta ce ta na ci-gaba da yin nazari a kan umarnin kotun.

Yanzu dai hukumar ta ce ta dakatar da shirin ba ‘yan takarar shahadar, har sai wani lokaci nan gaba da ba ta bayyana ba.

Jam’iyyar APC dai a jihar Zamfara ta na fama da rikici tun bayan zaben fidda gwani, wanda ta gudanar kafin babban zaben da aka gudanar a Nijeriya.

Leave a Reply