Mohammed Abba-Aji tare da Bukar Shuwa, na mazabar majalisar wakilai ta Jere sun garzaya kotun sauraron karrakin zabuka, a Maiduguri, wajen kalubalantar sakamakon da hukumar INEC ta nuna Kashim Shettima da Ahmed Satomi a matsayin wadanda suka lashe zabukan a Borno.

Joe Kyari Gadzama shi ne lauyan Abba-Aji, inda ya bayyana cewa wanda yake wakiltar ya kalubalanci sakamakon zaben ne bisa zargin murdiya tare da babakeren da ya gano a lokacin gudanar da zaben, wadanda suka ci karo da dokokin zabe.

Lauyan ya bukaci kotun sauraron koke-koken zaben da ta soke zaben tare da bayar da umurnin gudanar da wani ko ayyana wanda yake karewar a matsayin wanda ya samu nasarar zaben kujerar.

A tattaunawar sa da manema labarai a Maiduguri Sanata Abba-Aji,  ya bayyana dalilin da ya sa ya garzaya zuwa kotun saboda neman hakkin sa, biyo bayan gudanar da zaben mai cike da rashin tsari, a jihar Borno.

Ya ce zaben cike yake da karen tsaye a dokokin zabe da rashin bin ka’idoji, kuma zaben cike yake da rudani, wanda idan doka za ta yi aikin ta, dole a soke shi baki daya.