Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasenjo, ya bayyana ilimi yanzu a Najeriya a matsayin abin rudani.

Obasanjo, ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya halarci wani taro kan makamar ilimi na duniya da ya gudana birnin Dubai dake hadaddiyar daular larabawa.

Taron mai taken kawo sauyi a Najeriya, da yake amsa tambayoyin daga mahalarta taron tsohon shugaban kasa ya ce idan aka tambaye shi kan matsayin ilimi a Najeriya, abinda zai ce shi ne ana cikin rudani.

Ya ce idan ya yi misali da jihar sa ta Ogun, inda gwamnatin jihar ta mallaki jami’o’i 4, duk jami’ar da ka halarta a cikin su zaka gansu ne kamar makarantun sakandiri.

Obasanjo, ya ce sai dai yanzun yana ganin lokaci ya yi da za a yi gyara a bangaren darussan lissafi da kimiyya da kere-kere, da kuma al’adu domin samun cigaba.

Leave a Reply