Kungiyar tarayyar turai, ta yi tir da yadda ta’addanci da sayen kuri’u da kuma firgita jama’a su ka yi tasiri yayin gudanar da karashen zaben gwamnan jihar Kano.

Jami’an sa-ido na Kungiyar, sun ce hauragiya da tashin-tashina, da sayen kuri’u da kuma tada hankullan jama’a sun yi wa zaben jihar Kano dabaibayi tare da tasiri yayin gudanar shi.

Kungiyar ta bayyana damuwa a kan sakacin hukumar zabe da hukumomin tsaro musamman jami’an ‘yan sanda. na gaza magance matsalolin da aka fuskanta yayin gudanar da zaben.

A cikin rahoton da kungiyar ta fitar, ta ce wakilan ta sun shaida yadda ‘yan daba da sara-suka rike da makamai suka ci Karen su babu babbaka wajen firgitar da manema labarai da kuma masu kada kuri’u.

Ta ce ‘yan ta’ada sun muzguna wa al’umma, musamman a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa, tare da haifar da tarnakin da ya haramta wa ‘yan jarida gudanar da ayyukan su cikin tsanaki.

Leave a Reply