Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Filato bai kammala ba.

Babban Jami’in Zabe na Jihar kuma Shugaban Jami’ar Jihar Benue Farfesa Richard Kimbir ne ya yi wannan sanarwa a daren Lahadin da ta gabata.

Ya ce dole sai an samu ratar da za ta tabbatar da cewa kuri’un da aka jefa sun yi daidai da ratar da jam’iyyu biyun da su ka fi samun kuri’u ta nuna.

Gwamna Lalong na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 583 da 255, yayin da Jeremiah Useni na jam’iyyar PDP ya samu dubu 538 da 326.

Hukumar zaben ta ce, bambancin da ke tsakanin jam’iyyun biyu kuri’u dubu 44 da 929 ne, alhalin kuri’u dubu 49 da 377 ne aka soke.Ya ce za a sake zaben a kananan hukumomin da su ka hada da Jos ta Arewa da ta Kudu, da Kanam, da Langtang North, da Langtang South, da Mangu, da Panshin, da Kanke, da Mikang, da Quanpan, da Riyom, Shendam, da kuma Wase.“)}�07P1�

Leave a Reply