Rahotanni na cewa, yanzu haka jihar Benue ta shiga jerin jihohin da sai an sake zabe a wasu wuraren da ba a yi ba ko kuma aka soke zabukkan wuraren.

Bisa ga sakamakon da aka bayyana a jihar dai, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP kuma gwamna mai ci Samuel Ortom ya samu kuri’u dubu 410 da 576, yayin da Emmanuel Jimeh na Jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 329 da 22.

Sai dai kamar yadda dokar zabe ta gindaya, ba zai yiwu a tabbatar wa gwamna Ortom da nasara ba, saboda yawan kuri’un da aka soke sun fi yawan tazarar da wanda ya yi nasara ya samu.