Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ce matakin da jam’iyyar APC ta dauka na zakulo Sanata Ahmad Lawan, zabi ne kawai na jam’iyya ba wai an nada shi ba ne.

Ali Ndume ya yi kira ga ‘yan’uwan sa da jam’iyyar APC cewa su bi tsarin mulki da dokar Nijeriya wajen zaben wadanda za su rike ragamar majalisa a wannan karo.

Sanatan ya bayyana haka ne, yayin wata hira da ya yi da Jaridar Nigerian Tribune, inda ya gargadi jam’iyyar APC ta guje wa afkawa cikin irin rikicin da ta shiga a shekara ta 2015.

Sanata Ndume ya cigaba da cewa, jam’iyyar APC ta saba wa tsarin mulki wajen zabin da ta yi kwana nan.

Ya ce matakin da jam’iyyar APC ta dauka na zakulo Ahmad Lawan a matsayin dan takarar ta ya ba su mamaki, don haka ya ce ya kamata a ce APC ta zauna da ‘yan majalisar yankin domin su fito da duk wanda su ke so.

Leave a Reply