Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce har yanzu Nijeriya ta na fuskantar kalubale ta fuskar ciyar da kan ta da kuma sama wa kamfanoni kayan aiki ta hanyar noma.
Buhari ya bayyana haka ne, a wajen bikin bude kasuwar baje-koli ta kasa da kasa karo na 40 a Kaduna, inda ce kalubalen har yanzu ya na nan duk da cewa noma ya na taimakawa da kashi 25 da rabi wajen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.
Bikin baje-koli da ake gudanarwa a kowacce shekara, ya na gudana ne har tsawon kwanaki goma a karkashin cibiyar masana’antu, da albarkatun kasa da noma ta jihar Kaduna KADCCIMA, inda ake baje-kolin sana’o’i da fasahohin cikin gida da kasashen waje.
Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan masana’antu, da kasuwanci da zuba hannun jari Okechukwu Enelama, ya ce kulla hadaka tsakanin noma da masana’antu zai cike gibin da ake samu na karancin abinci da kayayyakin masarufi.
A cewar sa, Niyeriya na ci-gaba da fuskantar matsalar cimma bukatun ‘yan Nijeriya ta fuskar abinci, da kayayyakin da masana’antu ke bukata domin gudanar da ayyukansu.stev��ɱ�@



































