Kasar Amurka za ta ba mutumin da ya ba ta bayanai game da daya daga cikin ‘ya’yan marigayi Osama Bin Laden, kyautar dala miliyan daya kimamin naira miliyan 360 ke nan.

Hamza Bin Laden wanda ake nema ruwa a jallo shi ne shugaban wata kungiyar masu kaifin kishin Islama ta al-Qaeda, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Ana zaton yana rayuwa ne a kusa da iyakar kasar Afghanistan da Pakistan.

A ‘yan shekarun nan, ya saki wani faifan murya da bidiyo inda yake kiran mabiyan sa su kai wa kasar Amurka da sauran kasashen yamma hari a wani martani ga kisan mahaifin sa.