Direban jirgin saman da ya dauko dan wasan kwallon kafar nan Emiliano Sala, bai kammala karatun sa a makarantar horar da matukan jirgin sama ba.
Bincike ya nuna cewa David Ibbotson, wanda shine ya tuka jirgin da ya yi hatsarin bai da cikakken lasisin daukar fasinjoji wanda hakan ya jawo ake tantamar watakila ba a bi tsarin doka ba kafin jirgin ya tashi.
Har yanzu dai ba a gano gawar David, ba tun bayan da aka gano gawar dan wasan gaba na Cardiff City Emiliano Sala, a ranar 6 ga watan Fabrairu.
Wani rahoto da hukumar dake bincike a kan hatsarin jirgin sama ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa Mista Ibbotson mai shekaru 59 yana da lasisin tukin jirgi a Burtaniya da Amurka wanda hakan na nufin ba zai iya daukar fasinjoji ba tsakankanin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai.
Rahoton ya kuma bayyana cewa dole ne a gudanar da bincike domin sanin asalin Mista Ibbotson, da kuma tarihin aikin da ya gudanar a matsayin sa na matukin jirgin sama.
Jirgin saman dai ya yi batar dabo ne a ranar 21 ga watan Junairu dauke da dan wasan kwallon kafar wanda ya kammala shirye-shiryen komawar sa sabon kulob dinsa watau Cardiff daga Nantes.