Rahotannin na cewa, wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani jami’in hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa mai suna Mahadi Hassan a jihar Jigawa.

Shugaban sashen wayar da kai da hulda da jama’a na hukumar a jihar Jigawa John Kaiwa ya tabbatar da hakan a gidan talabijin na Channels, inda ya ce an yi garkuwa da Hassan ne tun ranar Juma’ar da ta gabata a kan hanyar zuwa Gwiwa da ke jihar.

Haka kuma, rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce har yanzu babu wani korafi da hukumar zabe ko iyalan wanda aka yi garkuwar da shi su ka gabatar mata ba.

Sai dai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bala Zama, ya tuntubi kwamishinan zabe na jihar Dakta Mahmooud Isah, inda ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun tuntubi iyalan jami’in hukumar zaben a kan batun kudin fansa.

Leave a Reply