Wasu ‘yan bindiga sun tarwatsa taron bikin kamun kifi na Dankwo da ake gudanarwa duk shekara a garin Lokoja bayan sun bude wa mahallarta taron wuta.
Rahotanni sun ce an fara bikin ne da misalin tsawon sa’a guda, yayin da ‘yan bindigar su ka kai farmakin, inda ake bikin a rafin Kabawa cikin kwale-kwale mai inji.
‘Yan bindigar da su ka tinkari wajen su uku a cikin kwale-kwale, sunyi ruwan harsasai a cikin taron, lamarin da ya sa al’umma su ka fara tserewa, yayin da su ka harbi mutane biyar.
An sanar da jami’an ‘yan sanda nan take sai dai kafin su iso wurin ‘yan bindigan sun tsere a cikin kwale-kwalen da suka taho.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kogi DSP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce duk mutane biyar da su ka jikkata su na nan da ran su su na karbar magani a cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Lokoja.
Ya ce babu wanda ya mutu sakamakon harin, kuma tuni an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kai harin.



































