Zababun ‘yan majalisar dokoki na jihar Sokoto na jam’iyyar APC 16, sun ki hallartar taron karbar takardan shaidar lashe zabe da hukumar zabe ta shirya a Sokoto.
A wajen taron, Hukumar zabe ta mika takardun shadar lashe zaben ga zababen gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, da mataimakin sa Mannir Dan’iya da wasu zababbbun ‘yan majalisar dokoki na jihar.
Sai dai zababbun ‘yan majalisun jam’iyyar APC ba su hallarci taron ba.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Sokoto Sambo Bello Danladi, ya ce akwai yiwuwar hare-haren da aka kai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar ne dalilin da ya sa su ka ki halartar taron.



































