Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP Peter Obi, ya ce babu kasar da za ta cimma matakin ci-gaba matukar ana aikata rashin gaskiya da magudi yayin zabubbukan ta.

Peter Obi, ya ce tafarki da kuma hanyar samun shugabanci nagari ne mafi a’ala, ta fuskar muhimmanci a madadin rawar da kowane shugaba zai taka a kan kujerar sa ta jagoranci.

Mista Obi wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Anambra, ya ce samun kujerar shugabanci ta tsarkakakkiyar hanya ita ce babbar madafa kuma ginshiki mai tushe na gaskiya da amana.

Ya ce aikata magudi da rashin gaskiya yayin zabe ya na daya daga cikin mafi kololuwar nau’ukan rashin adalci da ke da babbar nasaba da rashawa mai karya duk wata garkuwa ta ci-gaban kasa a siyasance da tattalin arziki.

Tsohon gwamnan, ya yi tsokaci game rashin gaskiyar da aka yi yayin zabubbukan kasar nan, cewa za su yi tasiri wajen cin karo da tsare-tsaren dimokuradiyya da kuma gurbata makomar kasa ta fuskar hana kai wa Tudun tsira.