Wadanda su ka sace Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim, sun nemi a biya makudan kudi kafin su sake shi kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Masu garkuwar dai, sun nemi a biya su Naira Miliyan 300 a matsayin kudin fansa idan har ana so su sako Malamin da wasu mutane 5 da aka sace su tare a ranar Alhamis da ta gabata.
An dai sace Malamin ne da wasu mutane 5 a kan hanyar Sheme zuwa Kankara da ke Jihar Katsina.
Wani makusancin Malamin Isma’il Bunyaminu ya bayyana wa manema labarai cewa, miyagun sun sa masu kudi har Naira Miliyan 300 kafin su sako Malaman.
Isma’il
Bunyaminu, ya ce Iyalin Malamin sun zauna game da lamarin, inda su ke neman
mutanen su rage kudin da su ka sa a tattaunawar da ake ci-gaba da yi da su.