Rabi’u Musa Kwankwaso , Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma Madugun Kwankwasiyya Injiniya
Rabi’u Musa Kwankwaso , Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma Madugun Kwankwasiyya Injiniya

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nesan ta kan sa da kuma jam’iyyar PDP a kan rikicin siyasar da ya faru a jihar Kano.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin ta hannun damar kwankwaso Binta Spikin, inda ta ce wasu daga cikin ;yan adawar kwankwaso ya ta yada jita-jitar ne domin su ba ta mashi suna.

Spikin ta ce a lokacin da kwankwaso ya ke gwamnan jihar kano, babban burin sa shine ya ga walwala da jin dadi ga al’ummar jihar, kuma hakan ne ya sa ya rika daukar ‘ya’yan talakawa zuwa kasashen waje domin karo karatu.

Idan dai ba a manta ba, kwanaki kadan kafin a sake zabe Kwankwaso ya fitar da sanarwa da ke cewa, mutanen jihar Kano su kwantar da hankalin su su yi zabe ba tare da tashin hankali ba.

A karshe ta yi kira ga magoya bayan Kwankwaso su zama ‘yan kasa na gari, saboda hakan ne zai daga darajar sunan su a idon duniya.