Jami’an ‘yan sanda a jihar Yobe sun bayyana rashin jin dadin su bisa ki biyansu alawus din abinci har na tsawon watanni hudu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ‘yan sandan mobile dauke da bindigu sun taru a gefen Bankin UBA a kusa da Central Roundabout a ranar Talatar da ta gabata, inda suka ce za su fara zanga-zanga a kan tituna idan gwamnati ba ta biya su hakokin su ba.
Daya daga cikin ‘yan sandan da bai bayyana sunan sa ba saboda wasu dalilai, ya ce rabon su da samun kudaden allawus din su tun watan Disambar shekara ta 2018.
Tun daga watan Disamban 2018, ba su biya mu allawus din cin abinci ba kuma babu wanda ke yi mana magana a kan lamarin.
‘Yan sandan sun bayyana takaicin su a kan yadda sauran jami’an tsaro irin sojoji da sauran su su ke samun allawus din su a kan lokaci, soboda haka su ke bukatar fadar shugaban kasa ta sani cewa, har yanzu ba a biya su hakokin su ba.