Adams Oshiomhole, Shugaban Jam’iyyar Ta APC Na Kasa
Adams Oshiomhole, Shugaban Jam’iyyar Ta APC Na Kasa

Jam’iyyar APC ta dage kan cewa, tilas ne jam’iyyar da ta ke da mafiya rinjaye a wakilan majalisar da aka zaba a wannan karon, kar su bari ‘yan adawa su karbe muhimman mukaman majalisar.

Shugaban jam’iyyar ta APC na kasa Adams Oshiomhole ne ya bayyana hakan a wajen liyafar cin abinci da shugaban kasa Buhari ya shiryawa dukkanin sabbi da tsaffin wakilan majalisar ta Dattawa da kuma wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Oshiomhole ya bayyana cewa, makasudin shirya liyafar shi ne a tsara yadda za a yi da batun shugabancin majalisar, domin tabbatar da ba a sanya ‘yan adawa a mahimman mukaman majalisar ba a wannan karon.

Ya kuma kara da cewa, jam’iyyar APC wacce ke da rinjaye da kimanin Sanatoci 65 da kuma ‘yan majalisar wakilai 223 daga cikin 360 da majalisar ta ke da su, tana da ikon daukan duk wata shawara ba tare da tilas sai ta sami goyon baya daga ‘yan adawa ba.

Saboda haka ya ce akwai bukatar jam’iyyar da ‘ya’yan su yi dubi da kyau, domin sun dauki darasi a kan abunda ya faru a shekara ta 2015.

Leave a Reply