Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta sanar da shirin shiga
yajin aikin gargadi na kwanaki 7 domin tilastawa gwamnatin
tarayya magance matsalar karancin takardun Naira da man
fetur.
A wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun shugabanta Joe
Ajaero da babban sakataren ta Emmanuel Ugboaja, kungiyar
ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo karshen
matsalar da ake ciki.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, matakin ya biyo bayan
taron kolin da kungiyar ta gudanar, wanda ya kaiga tsunduma
yajin aikin gargadin domin tilastawa gwamnati daukar
matakin magance matsalar.
Ta ce gaza wadata al’umma da takardun kudin Naira ya jefa
jama’a cikin matsin rayuwa, yayin da karancin man fetur ya
sake tsawwalla matsin rayuwar da ‘yan Nijeriyar ke fama da
shi.





































