Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi watsi da zargin
cewa ba ya tausaya wa talakawan Nijeriya, ya na cewa babu
wata gwamnati a tarihin baya-bayan nan da ta bullo da tsare-
tsaren tattalin arziki domin tallafa wa masu rauni kamar
gwamnatin shi.

Buhari ya bayyana haka ne, a cikin wata sanarwa mai taimaka
ma shi ta fuskar yada labarai Garba Shehu inda ya umurci
babban bankin Nijeriya da ministan shari’a su mutunta
umurnin kotu game da amfani da tsofaffin takardun Naira.

Tun farkon dai sanarwar ta ce babban bankin Nijeriya ba ya
bukatar umurni daga shugaban kasa kafin ya yi biyayya ga
hukuncin kotu.

Kwanan baya dai kotun koli ta yanke hukuncin cewa, a cigaba
da amfani da tsofaffin kudaden tare da sabbin da aka sauya wa
fasali har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Leave a Reply