Shugabannin kasashen Nihiyar Afrika, da su ka hada da Senegal da Ghana da Zimbabwe da kuma Nijar, sun aiko da sakon taya shugaba Buhari murnar samun nasara a zaben shekara ta 2019.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya ce shugabannin kasashen 3, sun aika sakon taya shugaba Muhammadu Buhari murna, sakamakon sake lashe zaben da ya yi.

Femi Adesina, ya ce Nana Koffi-Addo na kasar Ghana, da Mahamadou Issoufou na Jamhuriyyar Nijar, sun aiko wa shugaba Buhari sakon musamman, su na taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa da aka yi a Nijeriya.

Adesina ya kara da cewa, shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya taya shugaba Buhari murnar sake samun damar ci-gaba da shugabancin Nijeriya na wasu shekaru 4.

Shugaban kasar na Zimbabwe ma ba a bar shi baya ba, inda ya yi wa shugaba Buhari addu’ar iya sauke nauyin da mutanen Nijeriya su ka dora mashi.