Fitaccen Malami Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya shawarci Atiku Abubakar ya tabbatar ya garzaya kotu domin kwatar hakkin sa.

Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana haka ne, a cikin wata budaddiyar wasika da ya rubuta a shafin sa na Facebook, inda ya yi kira ga Atiku kada ya kuskura ya amince da sakamakon zaben da hukumar zabe ta sanar, wanda ya bayyana a matsayin na bogi.

Idan dai ba a manta ba, shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

 Don haka malamin ya bukaci Atiku ya garzaya kotu ya nemi hakkin sa, domin a cewar sa, shugaba Buhari ya yi amfani ne da karfin iko wajen yin magudin zabe.

A karshe Gumi ya yi kira ga gwamnati ta tabbatar ta saki duk mutanen da ta kama da sunan siyasa.