Jam’iyyar PDP, ta bayyana kwarin-gwiwar cewa za ta lashe duk zabubbukan gwamna da za a sake a wasu mazabu da rumfuna ko kananan hukumomi a fadin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar, ya ce duk wani kokarin da za a yi domin murde zaben ko karfa-karfa tare da magudi jama’a ba za su yarda da shi ba.

Ya ce abin kunya ne a ce, bayan kammala zabe APC ta fito ta na kukan yadda abubuwa su ka dagule masu, alhalin kowa ya ga yadda ta yi amfani da karfin sojoji wajen gudanar da zabe.

Kola Ologbondiyan, ya ce PDP ta na da yakinin cewa za ta yi nasara a dukkan zabukan da hukumar zabe ta ce ba su kammalu ba.

Da ya ke tsokaci a kan zaben jihar Rivers kuwa, Kola ya ce a can ma tamkar ture-kaza-kwashe-kwai jam’iyyar PDP za ta yi, domin kafin a dakatar da tattara kuri’u PDP ta na kan gaba da kuri’u dubu 81,000.

Ya ce a jihar Kano kuma kowa ya san tarihin al’ummar jihar ba su yarda su zabi mai wuwure kudaden talakawan su, kuma ba a yi musu wata barazana ko bude ido.