Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta tura wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sabon dogarin da zai ba shi kariya Idris Kassim Ahmed.

Wata majiya ta ce, an hangi sabon dogarin a fadar shugaban kasa ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da ya ke tsaron shuagaba Buhari a lokacin da ake gudanar da sallar Juma’a da kuma bayan kammala ta.

Idris Kassim dai ya maye gurbin tsohon dogarin shugaba Buhari Bashir Abubakar, wanda shugaba Buhari ya zaba a matsayin dogarin sa bayan cin amanar da tsohon dogarin sa Abdulrahman Mani ya yi masa.

Majiyar ta cigaba da cewa, tsohon dogarin Bashir Abubakar, shi ne mataimakin daraktan hukumar DSS reshen jihar Bayelsa, an turashi karo ilimi ne a jami’ar Buenos Aires da ke kasar Ajantina.

Leave a Reply