Majalisar dattawa ta dage zama domin karrama wani dan majalisar wakilai Temitope Olatoye da ya mutu a lokacin zaben gwamna da na majalisun jihohi a birnin Ibadan na jihar Oyo.
An dai koma zaman Majalisar ne da misalin karfe 10.50 na safe, inda Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya bude taro da addu’a kafin ya karanto zaman majalisar na ranar 26 ga watan Fabrairun da ya gabata.
An gabatar da bayanan zaman a lokacin da Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Ahmad Lawan ya sanar da mutuwar dan majalisar, sannan ya nemi a karrama shi ta hanyar yin shiru na tsawon minti daya.
Ahmed Lawan, ya kuma nemi a dage zaman majalisar kamar yadda ya ke a al’adar majalisar dokoki ta kasa domin karrama marigayin.