Wasu ‘yan bindiga sun tare wata mota dauke da wani injiniya dan kasar waje, inda su ka yi garkuwa da shi tare da harbe direban da ke tuka shi.

Wadanda abin ya faru kan idon su da rundunar ‘yan sanda ta jihar Jihar Kano sun tabbatar da faruwar lamarin.

Wani shaidun gani da ido, ya ce abin ya faru ne da misalin karfe 7:40 na safiyar Talatar nan.

Direban da aka harbe dai ya na aiki ne a kan titin kusa da shataletalen Dangi, inda ake aikin titi da gada a daidai mahadar Titin Gidan Zoo da Titin Zaria.

Har zuwa yanzu dai ba a tantance sunan wanda aka sace ba, kuma ba a san ko dan wace kasa ba ne.