Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta yi
alƙawarin miƙa dukkanin kayan zaɓen da jam’iyyun adawa za
su buƙata ba tare da ɓata lokaci ba.
Shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu,
ya ce hukumar ba ta da wani abu da za ta ɓoye a zaɓen da ake
taƙaddama a kan sa.
Jam’iyyun PDP da Labour dai su na son duba kayan zaɓen ne,
domin su samu damar shirya wa ƙarar da za su shigar ta
ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Idan dai baa manta ba, Jam’iyyar Labour ta yi barazanar
shirya zanga-zanga ta ƙasa baki ɗaya idan hukumar zabe ta
hana ta duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaben
shugaban kasa.