Wani karamin jirgin horars da dalibai na makarantar koyar da tukin jirgin sama na Nigerian College of Abiation Technology dake Zariya ya fado a kusa da wani kauye dake karamar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da aukuwar hatsain, wata sanarwa da jami’in yada labarai na makarantar Balarabe Palladan, ya sanya wa hannu, hukumar makarantar ta ce, jirgin kirar TB-9 ya fadi ne a yankin Birnin Gwari, bayan ya tashi daga filin jirgin sama na Kaduna.

Sanarwa ta kuma ce dukkan wadanda suke a cikin jirgin sun tsira da rayukan su, kuma tuni a ka sanar da hukumar bincike da tantance hatsarin jiragen sama ta kasa ’Accident Investigation Bureau (AIB)’ kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply