Shugaban Faransa Emmanuel Macron ba zai halarci taruruka da addu’o’in cika sekaru 25 da barkewar kisan kiyashin kasar Rwanda da za a yi ranar 7 ga watan afrilu mai zuwa ba.

Sakamakon kusancin da aka samu tsakanin Faransa da Rwanda bayan hawan Macron karagar mulki, wannan ya sa gwamnatin Rwanda aike wa shugaban da goron gayyata domin ya halarci wadannan adu’o’i da za a yi a birnin Kigali, to sai Macron, ya ce zai tura wani dan majalisar dokokin kasar mai suna Herve Berville, domin ya wakilce shi.

Herve Berville, maraya ne da ya tsira daga kisan kiyashin da aka yi 1994, kafin dauke shi zuwa Faransa lokacin yana da shekaru 4 a duniya.

Shugaban Rwanda Paul Kagame, ya share tsawon shekaru yana takun-saka da mahukuntan Faransa, bisa zargin cewa suna da hannu a wannan rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 800, mafi yawan su ‘yan kabilar Tutsi marasa rinjaye ne a kasar.