Akalla mutane 60 ne suka rasa rayukan su sakamakon hadarin da wasu motocin daukar fasinja biyu suka yi a yankin Bono da ke kudu maso gabashin kasar Ghana.

Mai magana da yawun ‘yan sandan kasar ta Ghana Joseph Antwi Gyawu, ya ce motocin sun yi taho mu-gama ne da misalin karfe biyu na daren.

Bayanai sun ce bayan da motocin suka yi taho mu-gama, nan take daya daga cikin su ta kama da wuta, bayan kowace mota na dauke da fasinjoji  50 a cikin ta.

Kwame Arhin, likita a asibitin gwamnati da ke garin Kintampo kusa da inda lamarin ya faru, ya ce yanzu haka akwai mutane 28 da aka kwantar a asibitin don kula da su sakamakon raunukan da suka samu.

A shekara ta 2016 ma, wata motar fasinja ta yi taho mu gama da wata motar daukar kaya a kan hanyar Tamale, inda mutane 53 suka rasa rayukansu.