Sadiya Umar Farouq, Minister of Humanitarian Affairs, Disaster Management And Social Development
Sadiya Umar Farouq, Minister of Humanitarian Affairs, Disaster Management And Social Development

Gwamnatin tarayya ta yi Allah-Wadai da matakin da kasar Kamaru ta dauka na dawo da ‘yan Nijeriya dubu arba’in da rikicin Boko Haram ya kora daga muhallan su a yankin karamar hukumar Rann ta jihar Borno.

Ta ce sai da ta roki alfarmar kasar Kamaru kada ta dawo da masu gudun hijirar sakamakon raba su da muhallan su da Boko Hama ta yi a Rann.

Shugabar hukumar lura da ‘yan gudun hijara Sadiya Farouq ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce sai da gwamnatin Nijeriya ta nemi alfarmar kasar Kamaru da kada ta kori ‘yan gudun hijirar yayin da ta yi barazanar korar su a baya.

Sadiya Farouq ta cigaba da cewa, gwamnatin tarayya ta ofishin ma’aikatar harkokin waje za ta dauki matakan da su ka dace a kan wannan lamari.

Leave a Reply