An bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a wannan Asabar din da ta gabata, bayan rufe wasu rumfunan zaben da aka gudanar da zaben.
Jami’an Hukumar INEC suka fara bayyana sakamakon zaben bayan kammala kada kuri’u a mazabun da ke karkashin kulawar su.
Miliyoyin ‘yan Najeriya ne suka kada kuri’un su a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayyar Nijeriya, domin zaber shugabanni da za su jagorance su har na tsawon shekaru 4 masu zuwa.
Sai
dai hankula sun fi karkata a shugaba kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da
kuma babban abokin hamayrsa na jam’iyyar PDP Atuku Abubakar, wannda ake saran
nan gaba kada hukumar zabe mai zaman kata ta kasa INEC zata bayyana wanda ya yi
nasara a cikin su.