Rundunar soji ta ce ta gano yadda wasu masu madafun iko a jihar benue ke haddasa rikici da daukar nauyin hare-haren da ake kai wa al’ummomin jihar.

Ta ce hakan bai zo da mamaki ba, duba da irin harin da aka kai garin Agatu ana mako daya kafin zaben shugaban kasa, da kuma harin Yammacin garin Gwer.

Rundunar ta ce ta fadada ayyukan ta a kan titin Loko zuwa Agatu, da Kwande da kuma iyakar garuruwan Benue, domin dakile hare-hare a nan gaba.

Kwamandar rundunar Atisayen ‘Whirl Stroke’ Manjo Janar Adeyemi Yekini ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya karanta yayin wani taron manema labarai a Makurdi.

Ya ce ire-iren wadannan masu madafun ikon, su ke kara rura wutar rikici a garuruwan kamar yadda aka gani a lokutan baya, a kan irin hare-haren da ake kaiwa jihar gabanin zaben shugaban kasa.

Leave a Reply