Atiku Abubakar, Former Vice President
Atiku Abubakar, Former Vice President

Kotun saurarem korafe-korafen zaben Shugaban kasa ta amince da bukatar jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar ta neman izinin mika wa shugaba Muhammadu Buhari sammaci ta hannun jam’iyyar APC.

PDP da Atiku Abubakar dai sun shigar da karar ne a farkon watan nan, inda su ke kalubalantar nasarar shugaba Buhari a zaben shugaban kasa da ya gabata.

Mai shari’a Abdul Aboki da ja jagoranci zaman kotun, ya yi umurnin cewa ana iya mika wa shugaba Buhari takardar tsammacin ta hannun kowane jigon APC a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Rahotanni sun ce, kotun daukaka kara da ke zama a Abuja za ta fara sauraren korafi da jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar su ka gabatar mata.

Atiku Abubakar dai, ya na ci-gaba da nuna rashin amincewa tare da kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana ranar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019.

Leave a Reply