Cacar baki ta barke tsakanin jam’iyyun PDP da APC, bayan APC ta ba ‘ya’yanta umarnin mamaye dukkan mukaman majalisar dokoki na kasa saboda su ke da rinjaye.

Sai dai jam’iyyar PDP ta kalubanci umarnin, inda ta bukaci ‘ya’yanta su yi takarar kowane mukami da ke majalisar.

A shekara ta 2015 dai, jam’iyyar PDP ta shammaci jam’iyyar APC, inda Sanata Ike Ekweremadu ya samu kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa, yayin da mukaman shugabannin majalisun biyu su ka shiga hannayen da jam’iyyar ta ce ba su kwanta mata ba.

Jam’iyyar PDP, ta ce babu wata doka da ta hana ‘ya’yan ta su nemi shugabancin majalisun tarayya da sauran muhimman kwamitoci.

Sakateren jam’iyyar PDP Sanata Ummaru Tsauri, ya ce tsarin mulkin Nijeriya bai ce dole sai wane ko wane ba za su shugabanci majalisun ba.

Leave a Reply