Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron majalisar zantarwa ta kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Daga cikin mahalarta taron kuwa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, da ministar kudi Zainab Ahmed Shamsuna, da ministan man fetur Ibe Kachikwu, da ministan lafiya Isaac Adewole, da ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed, da ministan wasanni Solomon Dalung da ministan ayyuka, gidaje da lantarki, Babatunde Raji Fashola.

Akwai mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ministan aikin noma, Audu Ogbeh; ministan kasafin kudi, Udo Udoma; babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Munguno; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan gwamnati, Oyo Ita.

Sauran sun hada da ministan shari’a Abubakar Malami, da ministan tsaro Mansur DanAli, da minista sadarwa Adebayo Shittu, da karamin ministan Neja Delta, Heineken Lokpobri.

Majalisar dai ta kunshi dukkan ministoci da manyan masu ba shugaban kasa shawara, da masu magana da yawun sa, da shugabannin ma’aikatan fadar shugaban kasa da na gwamnati da sakataren gwamnatin tarayya.

Leave a Reply