Rabi’u Musa Kwankwaso , Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma Madugun Kwankwasiyya Injiniya
Rabi’u Musa Kwankwaso , Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma Madugun Kwankwasiyya Injiniya

Madugun Jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya nemi a sake zaben da aka yi na jihar Kano.

A hirar sa da manema labarai a gidan sa Kwankwaso,  ya ce babu wasu kuri’un da za a iya cewa an jefa balle a zauna zaman kirga su.

Kwankwaso ya ce gwamnatin jihar Kano tare da hadin bakin Babban Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda, Anthony Micheal, sun taimaka wajen bai wa ‘yan sara-suka goyon bayan saran jama’a da dama tare da hana su yin zabe.

Ya ce a wasu mazabun tun da sanyin safiya aka dangwale kuri’u, kafin ma masu jefa kuri’ar na hakika su isa wurin zaben.

Kwankwaso ya ce in banda ‘yan kalilan wurare da aka yi zabe, a cikin birni, gaba dayan Kano ba zabe aka yi ba, an yi magude ne tare da taimakon DIG Anthony Micheal.

Ya ce bai ga dalilin da duk wani mai hankali ya  yarda da shirmen da aka yi a Kano da sunan zabe ba.